Sunday, August 19, 2018

Takaitacen Tarihin

#KUNDIN_TARIHIN_TIJANIYYA#
----------------Kashi Na 01----------------

TAKAITACEN TARIHIN SHIGOWAN DARIKAN TIJANIYYA NIJERIYA

Tarihin yaduwar Tijjaniyya a Nijeriya yana komawa ga mutane uku wadanda suka dauki dawainiyar yada darikar. Wadan nan mutane su ne, Shaihu Maulud Fal, Shaihu Umar Alfuti da Shhaihu Sharif Muhammad wanda aka fi sani da lakabin Sharu Zangina.

• Shaihu Maulud Fal ya kasance daga cikin manyan ‘yan Tijjaniyya wadanda suka yi aiki sosai wajen yada darikar, musamman a arewaci da yammacin Afirka. Shi mutumin Muritaniya ne, amma ya yi tafiye-tafiye da dama. Ya wuce ta Kasar Hausa a kan hanyarsa ta zuwa aikin Hajji inda ya shigar da Modibbo Ahmadu Raje cikin darikar. Ahmadu Raje shi ne kakan galadiman Adamawa Muhammadu, kuma ijazar (takardar izinin shiga darikar) da Shaihu Fal ya rubuta masa da hannunsa har yau tana nan a adane a wurin zuri’ar Galadiman Adamawa.

•Shehu Umar Alfuti babban dan Tijjaniyya ne wanda a sakamakon kokarinsa darikar ta samu kafuwa a dukkan sassan Afrika ta yamma. Umar Alfuti ya karbi darikar daga hannun Shaihu Abdulkarim Nakil wanda shi kuma tun da farko ya karbo ta daga Shaihu Maulud Fal, wanda muka gabatar da ambatonsa. Umar Alfuti ya zo kasar nan a zamanin Sarkin Musulmi Muahmmad Bello dan Shehu. Ya zauna a Sakkwato na wani lokaci, ya auri diyar Sarkin Musulmi Bello, sa’an nan ya wuce zuwa Makka inda ya game da shugaban Tijjaniyya na wannan zamani, Shaihu Muhammad Gali, wanda ya nada shi mukaddami a darikar. A kan hanyarsa ta komowa daga Hajji, Umar Alfuti ya biyo ta garuruwan Kukawa, Bauchi, Zaria, Katsina da Kano. A ko wane gari ya sauka, ya kan yi kokari ya nema wa darikar magoya baya. Bayan rasuwar Sarkin Musulmi Muhammad Bello, Umar Alfuti ya koma garinsu, Futa Toro, wanda a yau yake cikin kasar Senegal.

• Shi kuwa Shaihu Zangina, wanda ake jin cewa yana daga cikin jikokin Shaihu Tijjani, ya kawo ziyara ne birnin Kano a zamanin Sarki Alu Maisango. Daga Kano ya wuce zuwa Zaria, kuma ya zarce har zuwa garin Lokoja a

No comments:

Post a Comment